Gwamnatin Amurka ta taya ’yan Najeriya murnar cika shekaru 66 da samun ’yancin kai, tare da sake jaddada aniyarta na ƙarfafa dangantakar diflomasiyya tsakanin ƙasashen biyu.
Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta bayyana cewa tana daraja alaƙarta da Najeriya, tare da yaba wa da tattaunawar da ƙasashen biyu suka gudanar cikin shekarar da ta gabata.
Amurka ta bayyana Najeriya a matsayin ƙasar da ke da muhimmiyar rawa a Afirka, musamman wajen inganta zaman lafiya da tsaro a yankin, da kuma bunƙasa tattalin arziki.
Ta ce ƙasashen biyu sun haɗu kan wasu muhimman batutuwa da suka haɗa da dimokuraɗiyya, ’yancin addini, kasuwanci, zaman lafiya da tsaro.
Gwamnatin Amurkan ta kuma bayyana fatan samun ci gaba da zaman lafiya, haɗin kai da wadata a Najeriya, tare da fatan ƙasar da al’ummarta za su ci gaba da samun ci gaba a shekaru masu zuwa.
