Hukumar Alhazai ta Kasa NAHCON ta ce Saudiyya ta ƙi amincewa da buƙatar ƙara yawan kujerun maniyyatan da za su gudanar da aikin Hajji a shekarar 2027.
Matakin na nufin Najeriya za ta samu guraben mahajjata 50,000 ne kacal a aikin Hajjin na shekara mai zuwa.
NAHCON ta bayyana cewa ta tattauna da Ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya domin neman ƙarin gurabe, sakamakon karuwar bukatar gudanar da aikin Hajji daga ‘yan Najeriya. Haka kuma, wasu hukumomin jin daɗin alhazai na jihohi sun nemi a kara musu yawan gurabe.
Sai dai hukumomin Saudiyya sun ƙi amincewa da buƙatar, inda suka danganta matakin da ƙarancin wurare, ƙalubalen gine-gine a wuraren ibadar Hajji da kuma manufar ƙasar na bin ƙayyadadden kaso da aka ware wa kowace ƙasa.
Shugaban NAHCON, Ambasada Ismail Yusuf, ya ce hukumar ta fahimci rashin jin daɗin da matakin zai iya haifarwa ga maniyyata, hukumomin alhazai na jihohi da sauran masu ruwa da tsaki.
Ya ce hukumar ta yi amfani da hanyoyin diflomasiyya da na aiki da ake da su wajen neman ƙarin gurabe, amma za ta mutunta matakin da hukumomin Saudi Arabiya suka yanke.
