Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya tarbi rukuni na huɗu na alhazan Jihar, a filin sauka da tashin jiragen sama na Malam Aminu Kano wadanda suka dawo daga Ƙasar Saudiyya bayan kammala aikin Hajjin shekarar 2026.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, inda gwamnan ya godewa Allah bisa ba su damar gudanar da aikin Hajji cikin nasara tare da dawowa gida lafiya.
Gwamna Abba ya yabawa Amirul Hajj kuma Sarkin Gaya, Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulkadir, bisa jagoranci nagari da sadaukarwar da ya nuna a tsawon lokacin aikin Hajjin, wanda ya taimaka wajen tabbatar da kyakkyawan tsari da kula da alhazan Kano a ƙasa mai tsarki.
Haka kuma ya jinjinawa Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Kano bisa yadda ta gudanar da ayyukan Hajjin cikin kwarewa da jajircewa.
Gwamnan ya ce kula da jin daɗi, tsaro da walwalar alhazan Kano na daga cikin muhimman abubuwan da gwamnatinsa ta sanya a gaba, yana mai nuna gamsuwa da rahotannin da aka samu kan yadda aka gudanar da aikin Hajjin bana.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Gwamna Yusuf na yin kira ga alhazan da suka dawo da su ci gaba da riƙo da darussan haƙuri, ladabi, sadaukarwa da tsoron Allah da suka koya a lokacin aikin Hajji.
