Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya raba takardun mallakar filaye fiye da dubu 1 ga nadaddun masu riƙe da muƙaman siyasa da ke aiki a gwamnatin sa, wadanda suka hadar da PA, SA, SSA, SR, SSR, domin karrama gudunmawar da suka bayar wajen ci gaban gwamnati.
Taron rabon takardun filayen wanda ya gudana a dakintaro na Coronation dake fadar gwamnatin Kano, gwamna Abba ya ce shirin wani bangare ne na cika alkawari da ta daukar musu saboda jajircewar su.
Gwamnan wanda sakataren gwamnatin Kano, Alhaji Faruk Umar Ibrahim ya wakilta, ya ce manufar rabon filayen ba wai dan a mallaka musu filaye bane kawai, har ma da rage matsalar ƙarancin gidaje da ƙarfafawa al’umma gwiwar su mallaki kadarori domin samarwa iyalansu makoma mai kyau.
A nasa jawabin, Kwamishinan ma’aikatar kasa da tsare-tsare ta Kano Abduljabbar Muhammad Umar, ya ce shirin wata babbar dama ce ta bunƙasa rayuwar al’ummar Kano, kuma filayen zai taimaka wa waɗanda suka amfana su fara shirin mallakar gidajen kan su.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito cewar, waɗanda suka karɓi takardun sun tabbatar da cewa filayen da aka basu, wata dama ce da za ta taimaka musu wajen tabbatar da makomarsu ta mallakar kadarori da kaucewa fadawa matsalar haya ta hanyar samawa iyalan su muhalli.
