Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU) ta bai wa mahukuntan Jami’ar Noma ta Tarayya da ke Zuru, a jihar Kebbi, wa’adin kwanaki 21 su cika wasu muhimman buƙatu da ta ce gwamnati da jami’ar sun gaza aiwatarwa.
Wa’adin ya fara aiki ne daga ranar 29 ga watan Yuli, bayan wani taron gaggawa da reshen ASUU na jami’ar ya gudanar.
A cikin wata sanarwa da shugaban reshen kungiyar, Danbauchi Senchi, ya fitar, ASUU ta zargi mahukuntan jami’ar da kin aiwatar da yarjejeniyar da Gwamnatin Tarayya ta cimma da kungiyar a shekarar 2025.
Kungiyar ta ce yarjejeniyar ta haɗa da ƙarin albashin malaman jami’o’i da kashi 40 cikin 100, tare da biyan wasu haƙƙoƙin da suka rage a baya.
Haka kuma, ASUU ta bayyana cewa duk da Gwamnatin Tarayya ta fitar da kuɗaɗen biyan Consolidated Academic Tools Allowance (CATA) na watanni biyar ga jami’o’in tarayya, malaman Jami’ar Noma ta Tarayya da ke Zuru ba su amfana da kuɗin ba.
Bugu da ƙari, kungiyar ta yi zargin cewa har yanzu jami’ar ba ta samu kuɗaɗen fara aiki daga Gwamnatin Tarayya ba, lamarin da ta ce na ci gaba da kawo cikas ga gudanar da ayyukan jami’ar.
Duk da waɗannan ƙalubale, ASUU ta ce malaman jami’ar sun ci gaba da gudanar da koyarwa, bincike da kuma ayyukan hidima ga al’umma.
Kungiyar ta buƙaci mahukuntan jami’ar da Gwamnatin Tarayya su gaggauta magance matsalolin kafin cikar wa’adin kwanaki 21, tana mai gargadin cewa idan ba a ɗauki mataki ba, za ta shiga yajin aiki.
