Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya yi alkawarin ƙoƙarin dawo da Nijar, Mali da Burkina Faso cikin ECOWAS idan aka zaɓe shi a 2027.
Atiku ya bayyana hakan ne a wata hira da BBC Hausa, inda ya ce Najeriya da sauran ƙasashen ECOWAS sun bi hanyar da ba ta dace ba wajen tunkarar Nijar, Mali da Burkina Faso bayan juyin mulkin soja da ya kai ga karɓar mulki da sojoji suka yi a ƙasashen.
Ya kuma ce zai yi la’akari da amfani da rundunar ECOMOG wajen ƙarfafa tsaron yankin da yaƙi da ta’addanci.
Ƙasashen uku sun fice daga ECOWAS ne bayan ƙungiyar ta yi barazanar ɗaukar matakin soji a Nijar biyo bayan juyin mulkin shekarar 2023, tare da buƙatar a dawo da tsarin mulkin dimokuraɗiyya a ƙasar.
