Hukumar hana fasa ƙwauri ta sa Kwastam ta ce ta kama dabbobi da tsuntsaye 48 da ake zargin an safarar su ba bisa ka’ida ba a kan hanyar Kano zuwa Daura.
A cewar sanarwar hukumar, jami’anta na shiyyar Kano da Jigawa ne suka gudanar da samamen a yammacin Talata, inda suka kuma kama mutane uku da ake zargi da safarar namun dajin.
Daga cikin dabbobin da aka kama akwai:
Caracal guda 4
Chimpanzee guda 4
Ƙananan birrai guda 2
Manyan birrai guda 7
Galagos (bush babies) guda 2
Honey badger guda 1
Albino alligators guda 2
Rock fowls guda 6
Civet cat guda 1
Greater bustard birds guda 19
Hukumar ta ce waɗanda ake zargin sun yi ƙoƙarin ba jami’an cin hanci domin su tsallake bincike amma jami’an suka ƙi amincewa.
Daga bisani, an miƙa dabbobin da waɗanda ake zargin ga ofishin kula da dabbobi da ke hedikwatar Kwastam domin ci gaba da bincike da ɗaukar matakin shari’a.
Kwastam ta ce samamen ya taimaka wajen daƙile wata hanyar safarar namun daji da ke barazana ga dabbobin da ke cikin haɗarin bacewa.
