Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC a zaɓen 2027, Atiku Abubakar, ya bayyana rashin amincewarsa da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa INEC, yana mai cewa ba shi da tabbacin hukumar za ta yi abin da ya dace a zaɓen shekara mai zuwa.
Atiku ya bayyana hakan ne ranar Juma’a yayin wata hira da BBC Hausa, inda ya zargi Gwamnatin Tarayya mai jagorancin jam’iyyar APC da yin tasiri a kan INEC.
Ya yi kira ga ’yan Najeriya da su fito da yawa domin kada kuri’unsu, su kare kuri’unsu, sannan su tabbatar da cewa an ƙirga kuri’un da suka ƙada.
Da yake magana kan batun G-100, Atiku ya musanta zargin cewa shi ne ke hana ƙawancen samun nasara, yana mai cewa zargin ba shi da tushe.
Ya ce yana daga cikin waɗanda suka fara yunƙurin kafa ƙawancen, kuma da dama daga cikin mutanen da suka fara tafiyar tare da shi har yanzu suna cikin ƙawancen.
“Wannan zargi ba shi da tushe. Ni, Atiku Abubakar, ina cikin mutanen da suka fara ƙoƙarin kafa wannan ƙawance, kuma da dama daga cikin waɗanda muka fara wannan tafiya tare har yanzu suna cikinsa,” in ji shi.
