Gwamnan Jihar Neja, Umaru Bago, ya sanya dokar hana fita ta tsawon sa’o’i 24 a faɗin Minna, babban birnin jihar, sakamakon rikicin da ya ɓarke a wasu sassan birnin.
Dokar ta fara aiki ne nan take bayan kammala sallar Juma’a ta yau, kuma za ta ci gaba da aiki har sai gwamnatin jihar ta bayar da umarnin janye ta.
A ƙarƙashin dokar, an umarci mazauna birnin da su kasance a cikin gidajensu tare da guje wa duk wata zirga-zirga da ba ta zama dole ba. Haka kuma, an umarci jami’an tsaro da su tabbatar da cikakken aiwatar da dokar tare da ɗaukar matakan da suka dace domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Matakin na gwamnatin jihar ya biyo bayan zanga-zanga da rikicin da ya faru a Minna ranar Alhamis, wanda ake danganta shi da mutuwar wasu mutane da ake zargin masu haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba ne.
Rahotanni sun ce mutanen sun mutu ne yayin da suke tsare a hannun Hukumar Tsaron Fararen Hula ta Najeriya (NSCDC) a Minna, lamarin da ya haifar da zanga-zanga da tashin hankali.
Gwamnatin Jihar Neja ta buƙaci mazauna Minna da su kwantar da hankalinsu tare da bin umarnin da jami’an tsaro za su bayar.
Ana sa ran gwamnatin jihar za ta fitar da ƙarin bayani kan halin da ake ciki da kuma matakan da za a ɗauka yayin da lamarin ke ci gaba da sauyawa.
