Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya kafa hukumar kula da wutar lantarki ta jihar Adamawa
Gwamnan ya ce kafa hukumar na daga cikin matakan da ake ɗauka domin inganta samarwa da rarraba wutar lantarki, tare da samar da tsarin da zai ba jihar damar kula da harkokin wutar lantarki yadda ya kamata
Hukumar za ta mayar da hankali kan tsara harkokin wutar lantarki a jihar, da sa ido kan ayyukan masu samar da makamashi, da kuma taimakawa wajen samar da ingantaccen tsarin da zai ƙara samun wutar lantarki ga al’umma da harkokin kasuwanci.
