Gwamnatin Kano ta gargadi masu neman aikin gwamnati da su yi hattara da wasu mutane da ake zargi da sayar da takardun ɗaukar aiki na bogi, tare da karɓar kuɗi daga jama’a bisa alkawarin samo musu aiki a ma’aikatun gwamnatin Jihar.
Daraktar yaɗa labarai ta ofishin Shugabar ma’aikatan gwamnatin Kano Ruƙayya Uba Sulaiman ce ta bayyana hakan, cikin wata sanarwa da ta fitar, inda ta bukaci al’umma da su da dinga tabbatar da sahihancin duk wani bayani da ya shafi ɗaukar ma’aikata ta hanyar sahihan kafafen sadarwar.
Sanarwar ta ce gwamnati ta samu rahoton cewa wasu mutane da ƙungiyoyi na yaudarar masu neman aiki da ikirarin cewa suna da damar samar da guraben aikin gwamnati, sai dai ofishin shugabar ma’aikatan ya jaddada cewa takardun ɗaukar aikin gwamnatin Kano ba na sayarwa.
Sanarwar ta ce duk wanda ya nemi kuɗi ko wani abu domin samar da aikin gwamnati ga mutane, yana yin hakan ne ba tare da izinin gwamnati ba, kuma akwai bukatar masu neman aiki su guji mu’amala da su.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito ofishin Shugabar ma’aikatan na buƙatar jama’a da su kai rahoton duk wanda suke zargi da damfarar masu neman aiki, musamman masu sayar da takardun aiki na bogi, ga hukumomin da abin ya shafa.
