Jam’iyyar APC ta kafa babban kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027, wanda ya ƙunshi mutane 108.
Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Sanata Abdulaziz Yari, ne aka naɗa Darakta-Janar na kwamitin, yayin da Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma, zai kasance Sakataren kwamitin.
A wata sanarwa da Mai Magana da Yawun Shugaban Ƙasa, Bayo Onanuga, ya fitar ranar Asabar, an bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai jagoranci kwamitin a matsayin Shugaba, yayin da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, zai kasance mataimakinsa.
Haka kuma, Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, an naɗa shi a matsayin ɗaya daga cikin mataimakan shugaban kwamitin.
Sakataren Jam’iyyar na Ƙasa, Sanata Ajibola Bashiru, zai kasance Mataimakin Sakataren kwamitin, yayin da Hadiza Bala-Usman za ta zama Mataimakiyar Sakatariya.
A cewar sanarwar, Shugaba Tinubu ya buƙaci mambobin kwamitin da su yi aiki tuƙuru tare da haɗa kai, domin ganin jam’iyyar APC ta samu nasara a zaɓen shugaban ƙasa da aka shirya gudanarwa a watan Janairun 2027.
Shugaban ƙasar ya kuma umarci shugabannin sassa daban-daban na kwamitin da su tuntuɓi sauran ’yan jam’iyyar da ba a saka sunayensu cikin kwamitin ba, domin su ma su taka rawa wajen ayyukan yaƙin neman zaɓen jam’iyyar.
Kafa kwamitin mai mambobi 108 na nuna yadda APC ta fara ɗaukar matakan shirya tsaf domin tunkarar babban zaɓen 2027.
