Hukumomin shari’a a Turkiyya sun nemi daskarar da dukkan kadarorin tsohuwar ministar harkokin iyali da jin daɗin jama’a, Fatma Betül Sayan Kaya, da mijinta, Ilyas Kaya, bisa zargin cin moriyar wani rikicin asusun zuba jari da ya jawo asarar miliyoyin daloli.
Ofishin babban mai shigar da kara na birnin Istanbul ne ya tabbatar da aika wasiƙa ga hukumomin da abin ya shafa, domin daskarar da kadarorin ma’auratan a matsayin wani ɓangare na binciken da ake gudanarwa kan harkokin kasuwannin hannayen jari da asusun zuba jari.
Zargin ya samo asali ne daga ikirarin wata jam’iyyar adawa ta ƙasar, wadda ta ce Kaya da mijinta sun zuba kimanin lira miliyan 63, kwatankwacin dala miliyan 1.3, a hannayen jarin wani kamfanin gine-ginen jiragen ruwa a watan Afrilu, kafin daga bisani su sayar da hannayen jarin da ribar da ta kai kusan lira biliyan 1.3, wato dala miliyan 26.5, a watan Satumba.
Jam’iyyar adawar ta yi zargin cewa lokacin da aka gudanar da hada-hadar ya nuna yiwuwar samun bayanan sirri kafin faduwar kasuwar hannayen jari, wadda ta faru a tsakiyar watan Satumba, sai dai har yanzu ba’a tabbatar da zargin ba, kuma Kaya ba ta amsa takamaiman zarge-zargen da ake yi mata ba.
Kaya, wadda ta riƙe muƙamin ministar iyali daga shekarar 2016 zuwa 2018, ta yi murabus daga muƙaminta na mataimakiyar shugabar jam’iyyar AK Party mai mulki a ranar 26 ga Satumba, tana mai cewa ta ɗauki matakin ne domin a gudanar da bincike cikin ’yanci da adalci. Shugaba Recep Tayyip Erdoğan ya amince da murabus ɗin nata.
Rikicin ya biyo bayan matsalar wasu asusun zuba jari da suka kasa biyan buƙatun masu neman cire kuɗaɗensu, lamarin da ya shafi dubban masu zuba jari tare da haddasa faduwar farashin hannayen jari a kasuwar Istanbul. Hukumomin Turkiyya sun ce ana ci gaba da bincike kan zargin maguɗi da almundahana a harkokin kasuwannin kuɗi.
