Shugaban Majalisar Wakilan Najeriya, Tajudeen Abbas, ya ɗauki nauyin rajistar fursunoni 120 na gidan gyaran hali ta kasa, da ke Abuja domin su rubuta jarrabawar NABTEB da NECO ta shekarar 2026.
An gudanar da rajistar ne a cibiyar gyaran hali ta da ke Kuje, Abuja, a wani ɓangare na ayyukan tunawa da cikar shugaban majalisar shekaru 61.
Da yake jawabi ta hannun mai ba shi shawara kan harkokin jin ƙai, David Igbe, Abbas ya ce wannan tallafi na daga cikin ƙoƙarinsa na tabbatar da cewa kasancewa a gidan gyaran hali bai zama shinge ga neman ilimi da gina rayuwar gaba ba.
A nasa ɓangaren, Kwanturola na gidan gyaran hali ta Abuja, Christopher Jen, ya bayyana ilimi a matsayin muhimmin ginshiƙi wajen gyara halayya, farfaɗo da rayuwar fursunoni da kuma shirya su domin komawa cikin al’umma.
Hukumar NCoS ta ce sama da fursunoni 2,000 a Abuja ne aka riga aka yi wa rajista domin shirye-shiryen ilimi daban-daban, yayin da waɗanda suka rubuta jarrabawar NABTEB da NECO ta shekarar 2025 suka samu sakamako mai kyau.
