Hukumar Inshorar Lafiya ta Ƙasa (NHIA) ta sanar da shirin fara biyan kashi 50 cikin 100 na kuɗin radiotherapy da ake yi wa masu fama da cutar kansa.
Daraktan-Janar na hukumar, Dakta Kelechi Ohiri, ya ce manufar shirin ita ce rage wa marasa lafiya da iyalansu nauyin kuɗin jinyar cutar kansa, tare da ƙara yawan mutanen da za su samu damar samun ingantacciyar kulawa.
Ya bayyana cewa hukumar na kuma aiki tare da cibiyoyin kula da masu fama da cutar kansa da kamfanonin magunguna domin inganta samar da magunguna da hanyoyin jinya.
Matakin na zuwa ne a lokacin da masu fafutukar yaƙi da cutar kansa ke ci gaba da wayar da kan jama’a kan muhimmancin gano cutar da wuri da kuma fara magani cikin lokaci.
Ƙungiyar wayar da kan jama’a kan cutar kansa, Women for Cancer Early Detection and Treatment Foundation, ƙarƙashin jagorancin Ambasada Halisa Muhammad, ta bayyana cewa irin wannan tallafi zai taimaka wajen rage nauyin kuɗin jinya da marasa lafiya da iyalansu ke fuskanta.
Masana harkokin lafiya na ci gaba da kira ga jama’a da su riƙa zuwa duba lafiyarsu da wuri, domin gano cutar kansa tun kafin ta yi kamari na ƙara damar samun nasarar magani.
