Sarkin Morocco Mohammed na shida ya naɗa mace ta farko a matsayin Firaministar ƙasar, kwanaki bayan da jam’iyyarta ta lashe zaɓen ‘yan majalisar dokoki.
Fatima Zahra Mansouri ta zama mace ta farko da aka naɗa a matsayin firanministan ƙasar, wanda Sarki Mohammed na 6 Morocco ya ɗaura wa nauyin kafa sabuwar gwamnatin.
Kunɗin tsarin mulkin Morocco ne ya bai wa sarki ƙarfin ikon zaɓa tare da naɗa firamninsta, amma wanɗa zai naɗa ya fito daga jam’iyyar da ta samu mafi rinjayen wakilai a majalisar dokoki.
Naɗin Mansouri na ranar Talata ya zo bayan da jam’iyyarsu ta PAM masu tsaƙa-tsaƙin ra’ayi ta lashe mafi rinjayen kujeru a zaɓen majalisar dokoki da ya gudana a makon jiya.
Yanzu Fatima Zahra ta zama mace ta biyu da ta rike muƙamin Firanminista a ƙasashen ɗaukacin ƙasashen labarawa, bayan Najla Bouden da ta jagorancin gwamnatin Tunisia tsakanin shekarar 2021 zuwa 2023.
Sabuwar gwamnatin da Mansouri za ta kafa za ta fuskacin ƙalubalen cika alkawuran da aka yi wa masu kaɗa kuri’a yayin yaƙin neman zaɓe, masaman rage hauhawan farashin kayayyaki, ƙarin albashin ma’aikata da kuma samar da ayyukan yi.
