Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya buƙaci al’ummar jihar da su rungumi zaman lafiya, hadin kai da mutunta juna yayin da ake tunkarar babban zaben 2027.
Gwamnan ya yi kiran ne a yayin bikin cikar Najeriya shekaru 66 da samun ’yancin kai, wanda aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha da ke ƙofar mata.
Gwamna Abba ya ce akwai buƙatar ’yan siyasa, shugabannin al’umma da sauran ’yan Najeriya, su guji tashin hankali, rarrabuwar kawuna, rashin hakuri da aikata laifuka, yana mai cewa zaman lafiya shi ne ginshikin ci gaban al’umma.
Gwamnan ya kuma yi kira ga al’ummar Kano da su yi addu’ar samun zabe mai inganci, cikin ’yanci da adalci, tare da sauke nauyin da ya rataya a kan su na kasancewar ‘yan kasa.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Gwamna Yusuf na cewa gina kasa na bukatar hadin kai da sadaukarwa, tare da mutunta bambancin harsuna, al’adu, addinai da ra’ayoyin juna, tare da tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da mayar da hankali wajen bunkasa ilimi, kiwon lafiya, noma, ababen more rayuwa, samar da ruwa, tsaro da tallafawa ‘yan jihar.
