Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, yayi maraba da sanya hannun gwamnatin tarayya a aikin bunƙasa noman rani na Dam ɗin Kafinchiri, yana mai cewa aikin zai taimaka wajen ƙara samar da abinci da inganta rayuwar dubban manoma.
Gwamna Yusuf ya bayyana haka ne yayin da ya kai ziyarar duba aikin tare da Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu, Abdurrahman Kawu Sumaila, a Dam ɗin Kafinchiri, wanda gwamnatin tarayya haɗin gwiwa da ta Kano ke wajen aiwatar da aikin.
Gwamnan ya ce madatsar ta kasance muhimmiyar madogara ga al’ummar yankin tsawon shekaru, musamman wajen noman rani da samar da shinkafa mai inganci gajihar Kano, sai dai sakamakon rashin kulawa da madatsar ta fuskanta tsawon lokaci, kusan kashi 90 cikin 100 na ƙarfinta ya daina aiki.
Da yake jawabi yayin ziyarar duba aikin Sanatan kano Kudu Abdurrahman Kawu Sumaila ya bayyana irin ayyukan da suka samo a fannin noman rani ta yadda al’umma za su anfana.
Wakilinmu Kamal Umar Kurna ya ruwaito Gwamna Yusuf na cewa irin ayyuka na Dam ɗin kafin ciri na daga cikin matakan da gwamnatinsa ke ɗauka domin bunƙasa sufuri, noma da tattalin arziki, tare da inganta rayuwar al’ummar Kano.
