Jam’iyyar NDC ta bayyana cewa tana tattaunawa da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) kan yiwuwar sauya ko gyara tambarin jam’iyyar gabanin zaɓukan 2027.
A wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙasa na jam’iyyar, Osa Director, ya fitar ranar Juma’a, NDC ta ce akwai wasu batutuwa da ya kamata a warware kafin a maye gurbin tambarin da take amfani da shi a yanzu da sabon tambarin da aka gyara.
Jam’iyyar ta bayyana cewa tana aiki tare da INEC domin tabbatar da cewa duk wani sauyi da za a yi kan tambarinta ya kasance cikin bin ƙa’idoji da dokokin hukumar zaɓe.
NDC ta ce tattaunawar da take yi da INEC na da muhimmanci domin kauce wa duk wata matsala da za ta iya tasowa dangane da tambarin jam’iyyar a lokacin zaɓukan 2027.
