Kwamitin Majalisar Wakilai da aka kafa domin binciken zargin kafa wata hukumar bogi ya wanke Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, daga zargin hannu a ayyukan hukumar.
Shugaban kwamitin, Yusuf Gagdi, ya bayyana cewa binciken da kwamitin ya gudanar bai gano wata hujja da ke nuna cewa Gbajabiamila ya kafa hukumar, ya amince da ita ko kuma ya shiga cikin ayyukanta ba.
Maimakon haka, kwamitin ya gano cewa Gbajabiamila ne ya kai rahoton lamarin ga jami’an tsaro da hukumomin bincike bayan an gabatar masa da ƙorafi kan ayyukan hukumar.
Kwamitin ya kuma gano cewa wata takarda da aka yi amfani da ita wajen nuna cewa an naɗa Prince Adeniyi Adeyemi a matsayin Darakta-Janar na hukumar an ƙirƙire ta ne, kuma ba ta fito daga Fadar Shugaban Ƙasa ba.
Binciken ya ƙara nuna cewa babu wata doka ko umarnin Shugaban Ƙasa da ya kafa hukumar da ake magana a kai.
