Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya yi Alla-wadai da hare-haren da ’yan bindiga suka kai wasu sassan ƙananan hukumomi huɗu na jihar, inda ya sha alwashin cewa gwamnatinsa za ta ɗauki matakan da suka dace domin ƙarfafa tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, inda sanarwar ta ce hare-haren sun shafi ƙananan hukumomin Garun Mallam, Rogo, Bebeji, da wasu al’ummomi da ke kewaye da Gwarzo.
Gwamna Yusuf ya jajantawa waɗanda hare-haren suka shafa, tare da bayyana lamarin a matsayin abin damuwa kuma wanda ba za’a amince da shi ba, tare da bada tabbacin cewa gwamnati za ta haɗa kai da hukumomin tsaro domin hana sake afkuwar hare-haren a nan gaba.
Gwamnan ya ce ya umarci hukumomin da abin ya shafa da su ƙara sa ido, tattara bayanan sirri da kuma inganta tsarin kai ɗaukin gaggawa a yankunan da lamarin ya shafa, tare da buƙatar mazauna yankunan su kwantar da hankalinsu tare da bai wa jami’an tsaro cikakken haɗin kai.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Gwamna Yusuf na yin kira ga jama’a da su rika bayar da sahihan bayanan da za su taimaka wajen gano waɗanda ke da hannu a hare-haren, haɗi da yabawa jami’an tsaro bisa ƙoƙarin da suke yi, tare da roƙonsu da su ci gaba da gudanar da ayyukan leƙen asiri domin kare al’ummomin da ke cikin haɗari.
