Gwamnatin Kano ta yi kira da a ƙara zuba jari a fannin ilimi, kiwon dabbobi da samar da hanyoyin samun sana’o’i, domin inganta rayuwar al’ummomin fulani da kuma bunƙasa tattalin arzikinsu.
Mataimakin Gwamnan Kano, Murtala Sule Garo, ne ya bayyana hakan yayin da yake wakiltar Gwamna Abba Kabir Yusuf a taron ƙungiyar Tabital Pulaaku International
Garo ya ce akwai buƙatar inganta harkokin kiwon dabbobi, samar da ruwan sha, kula da lafiyar dabbobi, samun jari da kasuwanni, tare da horar da matasa da mata sana’o’in dogaro da kai domin ƙara musu damar samun abin yi.
A ɓangaren tsaro kuwa, Garo ya buƙaci ƙara tattaunawa da fahimtar juna tsakanin manoma da makiyaya, tare da haɗin gwiwar sarakunan gargajiya, hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki, domin samar da zaman lafiya da kare rayuka da dukiyoyi.
Tun da farko a jawabin sa, Sarkin Kano Muhammad Sanusi II, jaddada buƙatar fayyace nauyin dake tsakanin shugabancin ƙungiyar fulanin na ƙasa da ƙasa da rassanta na ƙasashe daban-daban, domin mayar da hankali wajen tsara dabaru da daidaita ayyukan ƙungiyar.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Sarkin na cewa rassan ƙungiyar na ƙasashe daban-daban su ne ya kamata su ɗauki alhakin harkokin da suka shafi ƙasashen da suke wakilta, tare da yin aiki bisa tsarin da shugabancin ƙasa da ƙasa ya shimfiɗa.
