Jami’ar Al-Istiqama da ke Sumaila ta karrama marigayi Alhaji Aminu Alhassan Dantata da digirin girmamawa bayan rasuwarsa, saboda irin gudunmawar da ya bayar wajen tallafawa ilimi, kasuwanci da ci gaban al’umma.
An gudanar da karramawar ne a yayin bikin yaye ɗaliban jami’ar rukuni na biyu da na uku, inda aka gabatar da karramawar ga iyalan marigayin.
Da yake jawabi yayin gabatarwa da iyalan marigayin shaidar karramawar, Shugaban jami’ar Farfesa Abdulhadi Sale Kumurya ya ce Marigayi Aminu Dantata ya taka muhimmiyar rawa wajen tallafawa jami’ar tun farkon kafuwarta, musamman ta hanyar ɗaukar nauyin karatun ɗalibai 100 marasa galihu na tsawon shekaru huɗu.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Farfesa Kumurya na cewa gudunmawar marigayin ta taimaka wajen samar da damar karatu ga matasa, tare da rage ƙalubalen da wasu daga cikinsu ke fuskanta wajen samun ilimi mai zurfi.
