Wasu ’yan Najeriya na amfani da kuɗaɗen ajiyarsu, karɓar bashi da kuma sayar da wasu kadarori domin samun damar sayen hannun jarin Dangote Refinery a yayin da ake shirin fara sayar da hannun jarin kamfanin ga jama’a, wato IPO.
Rahotanni sun ce wasu masu sha’awar sayen hannun jarin na kallon shirin a matsayin wata dama ta mallakar wani kaso a cikin katafaren kamfanin matatar man.
Wasu daga cikin masu son shiga shirin sun bayyana cewa suna amfani da kuɗaɗen da suka tara tsawon lokaci, yayin da wasu kuma suka ce sun nemi rance ko sayar da wasu kadarorinsu domin samun kuɗin sayen hannun jarin.
Sai dai masana harkokin kuɗi sun yi kira ga masu son saka jari da su yi taka-tsantsan, su fahimci yadda kasuwar hannun jari take da kuma haɗarin da ke tattare da saka kuɗi, kafin yanke shawarar shiga jarin.
Shirin IPO na Dangote Refinery na zuwa ne a daidai lokacin da ake ƙara samun sha’awar ’yan Najeriya kan mallakar hannun jari a manyan kamfanoni, musamman kamfanonin da ke taka muhimmiyar rawa a tattalin arzikin ƙasar.
