Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasar Najeriya, Atiku Abubakar, ya buƙaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana dalilin da ya sa bai halarci babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na uku a jere ba.
A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai ya fitar, Atiku ya ce rashin halartar taron na tsawon shekaru uku a jere na buƙatar ƙarin bayani daga Fadar Shugaban Ƙasa.
Ya ce ya kamata Fadar Shugaban Ƙasa ta fayyace ko akwai wani dalili na musamman da ke hana Shugaba Tinubu zuwa Amurka, yana mai cewa ƴan Najeriya na da haƙƙin sanin dalilin da ya sa shugaban bai halarci taron ba.
Atiku ya bayyana taron Majalisar Ɗinkin Duniya a matsayin muhimmin dandali da shugabannin ƙasashe ke amfani da shi wajen tattauna batutuwan tsaro, kasuwanci, ci gaban tattalin arziki, saka hannun jari da haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa.
A cewarsa, duk da cewa Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, na iya wakiltar Najeriya, hakan bai kamata ya maye gurbin halartar Shugaban Ƙasa da kansa ba.
Haka kuma, Atiku ya yi tambaya kan rahotannin da suka ce an tanadar wa Shugaba Tinubu kujera kusa da Shugaban Amurka, Donald Trump, a yayin taron, amma daga baya bai halarta ba.
Tun daga shekarar 2024 zuwa 2026, Shugaba Tinubu bai halarci zaman babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya da kansa ba, inda a kowace shekara ya tura Mataimakinsa, Kashim Shettima, domin wakiltar Najeriya.
