Mataimakin Shugaban Ƙasar Najeriya, Kashim Shettima, ya jagoranci tawagar Najeriya zuwa birnin New York na ƙasar Amurka, domin halartar babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne ya umarci Mataimakin Shugaban Ƙasar da ya wakilce shi tare da jagorantar tawagar Najeriya a taron na bana.
Tawagar ta ƙunshi Gwamnan Jihar Rivers, Siminalayi Fubara; Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal; ministoci da sauran manyan jami’an gwamnatin tarayya.
Za a gudanar da muhawarar babban taron daga ranar 22 zuwa 28 ga Satumba 2026, ƙarƙashin taken “Restoring Trust, Managing Transformation: A United Nations That Delivers for All.”
A yayin taron, ana sa ran Mataimakin Shugaban Ƙasar zai gabatar da jawabin Najeriya, tare da bayyana matsayinta kan muhimman batutuwan da suka shafi zaman lafiya da tsaro, ci gaban tattalin arziki da haɗin gwiwar ƙasashe.
Haka kuma, Shettima zai halarci wasu taruka na manyan ƙasashe tare da gudanar da ganawar ƙasashe biyu-biyu da shugabannin ƙasashe, ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa da abokan hulɗar ci gaba.
Mataimakin Shugaban Ƙasar ya isa New York a ranar Litinin, inda ya bayyana cewa hulɗar Najeriya a taron za ta kasance bisa la’akari da muradun ƙasar da kuma ƙoƙarin ƙarfafa matsayinta a harkokin duniya.
