Rundunar sojin kasar nan ta ceto ɗalibai mata shida na jami’ar rarayya da ke Dutsin-Ma, tare da wani direban mota, waɗanda ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a jihar Katsina, rundunar ta ce an ceto mutanen bakwai ne a wani samame da sojoji suka gudanar.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a hanyar Daye zuwa Malumfashi, da ke ƙaramar hukumar Danmusa, bayan wasu ’yan bindiga sun kai hari kan motar kasuwanci da ke tafiya daga Kaduna zuwa Katsina.
Sojojin da ke ƙarƙashin rundunar Operation FANSAN YAMMA, sashe na biyu, sun garzaya wurin bayan samun kiran neman agaji, isowarsu cikin gaggawa ta tilasta wa maharan tserewa tare da barin mutanen da suka yi garkuwa da su.
Daga cikin waɗanda aka ceto akwai ɗalibai mata shida na jami’ar tarayya da ke Dutsin-Ma, da kuma direban motar kasuwanci, rahotanni ba su bayyana ko waɗanda ake zargi da aikata garkuwar an kama su ba.
Rundunar sojin ta ce tana ci gaba da gudanar da ayyukan tsaro a yankin domin kare al’umma da ceto waɗanda aka yi garkuwa da su, tare da dakile ayyukan masu aikata laifuka a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.
