Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya taya Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Bola Tinubu, murnar cika shekaru 66 da Haihuwa.
A cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labaran sa, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, Gwamna Yusuf ya bayyana Oluremi Tinubu a matsayin shugaba mai tausayi da kishin ƙasa, wadda gudunmawarta ke taimakawa wajen aiwatar da ajandar gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Gwamnan ya yaba da irin ƙoƙarin da Uwargidan Shugaban Ƙasar ke yi wajen inganta rayuwar mata, yara da sauran masu ƙaramin ƙarfi, musamman ta fannonin ilimi, kiwon lafiya, ci gaban al’umma da tallafa wa tattalin arzikin jama’a.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Gwamna Abba na cewa shirye-shiryen da take aiwatarwa na samar da damarmaki da inganta rayuwar al’umma na ƙara taimakawa wajen cimma manufofin gwamnatin tarayya.
