Gwamnatin jihar Plateau ta sanya dokar hana fita daga magariba zuwa wayewar gari a ƙananan hukumomin Barkin Ladi, Bokkos da Mangu, sakamakon sabbin hare-haren da suka yi sanadin mutuwar mutane.
Kwamishiniyar yaɗa labarai da sadarwa ta jihar, Joyce Ramnap, ce ta sanar da matakin a wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin, inda ta ce dokar za ta fara aiki nan take daga ƙarfe shida na yamma zuwa shida na safe, har sai an bada wani sabon umarni.
Gwamnatin ta bayyana cewa an ɗauki matakin ne domin tabbatar da zaman lafiya, kare rayukan jama’a da bai wa jami’an tsaro damar daidaita al’amura a yankunan da abin ya shafa.
Rahotanni sun ce aƙalla mutane 9 ne aka kashe a wasu hare-hare daban-daban da suka faru tsakanin daren Asabar da safiyar Lahadi a wasu sassan jihar Plateau, hukumomin tsaro sun samu umarnin tabbatar da bin dokar hana fita.
Baya ga dokar hana fita, gwamnatin jihar ta kuma haramta amfani da babura a cikin ƙananan hukumomin uku, ta buƙaci mazauna yankunan su tsara harkokinsu yadda za su kammala zirga-zirgarsu kafin fara dokar da ƙarfe shida na yamma.
