
Ishaq Sani Dambazau
Gwamnatin Tarayya ta yi watsi da sukar da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi kan rashin halartar Shugaba Bola Ahmed Tinubu taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81 da ake gudanarwa a birnin New York na Amurka.
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ya ce adawar siyasa da muhawara a bainar jama’a na daga cikin abubuwan da dimokuraɗiyya ta amince da su, amma bai kamata a gabatar da hasashe a matsayin tabbataccen bayani ba.
Martanin gwamnatin ya biyo bayan kalaman Atiku da wata ƙungiyar masu fafutukar siyasa da ke Amurka, waɗanda suka yi tambaya kan dalilin da ya sa Tinubu bai halarci taron Majalisar Ɗinkin Duniya ba a karo na uku a jere.
A halin yanzu, Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya isa birnin New York domin wakiltar Tinubu da jagorantar tawagar Najeriya. Ana sa ran zai gabatar da jawabin ƙasar a babban taron, tare da halartar wasu muhimman tarurruka da ganawa da shugabannin ƙasashe.
Gwamnatin Tarayya ta jaddada cewa rashin halartar Tinubu ba ya rage matsayin Najeriya a fagen diflomasiyya, tana mai cewa Shettima na wakiltar shugaban ƙasa da cikakken iko. Ta kuma bayyana cewa Tinubu yana hutun shekara kuma Najeriya za ta samu cikakkiyar wakilci a taron.
