
Ishaq Sani Dambazau
Jam’iyyar ADC ta ce hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke kan zaɓukan shugabannin jam’iyyar a jihohi bai shafi ƴan takarar da ta tsayar domin shiga zaɓe ba.
Jam’iyyar ta bayyana cewa hukuncin kotun ya shafi batun zaɓen shugabannin jam’iyya daga matakin gunduma zuwa ƙananan hukumomi da jihohi ne kawai, ba zaɓen fidda gwani da aka yi na fitar da ƴan takararta ba.
Sakataren yaɗa labarai na ƙasa na jam’iyyar, Mallam Bolaji Abdullahi, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar jim kaɗan bayan sanar da hukuncin kotun.
Abdullahi ya ce hukuncin ba shi da wani tasiri kan ƴan takarar da jam’iyyar ta tsayar a dukkan matakai, inda ya yi kira ga mambobi da magoya bayan jam’iyyar da su kwantar da hankalinsu.
Jam’iyyar ta kuma bayyana cewa ta fara shirin ɗaukaka ƙara kan hukuncin, saboda ba ta amince da shi ba, domin a cewarta hakan bai yi daidai da doka ba.
Jam’iyyar ta ce za ta ci gaba da bin hanyoyin doka domin kare matsayinta, tare da tabbatar da burinta na samar da wata dama ga ƴan Najeriya.
