
Aminu Abdullahi Ibrahim
An kammala Maulidin Shehu Ahmad Tijjani karo na 69, a nan Kano inda Halifa Sheikh Hassan Sani Kafinga, ya jagoranci gabatarwa.
An kammala maulidin wanda ya samu halartar manyan mutane daga ciki da wajen kasar nan a ranar Alhamis.
Sheikh Khalifa Hassan Sani Kafinga ya ce Darikar Tijjaniyya ba bidi’a ba ce, illa wata hanya ce ta koyar da addinin musulunci bisa koyarwar Alkur’ani mai girma da sunnar manzon Allah.
Ya ce tun kafuwar darikar, manufarta ita ce karfafa bautar Allah, tarbiyya ta gari da kuma riko da koyarwar musulunci kamar yadda Alkur’ani da Sunnah suka tanada.
Ya kara da cewa gina darikar Tijjaniyya ne a kan manyan ginshikai guda uku, wadanda ke jagorantar mabiyanta wajen gudanar da ibada, kyautata dabia da kuma kusantar Allah.
A jawabinsa Khalifa Darikar Tijjaniya sarkin Kano Muhammadu Sanusi da ya samu wakilcin ya bukaci al’umma su rinka koyi da magabata.
Shi ma gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, da ya samu wakilcin kwamishinan addinai Sheikh Ahmad Tijjani Auwalu, ya taya mabiya darikar tijjaniya murnar zagayowar ranar Maulidin, tare da yin kira a gare su su karfafa addu’o’in samun zaman lafiya da cigaba mai dorewa.
Daya daga cikin manyan baki Malam Nura Hussain ya yi kira ga al’ummar Musulmi da su karfafa haɗdin kai, zaman lafiya da riko da koyarwar Alkur’ani da Sunnah.
