Kungiyar Malaman Jami’o’i, ASUU, reshen Jami’ar Sule Lamido da ke Kafin Hausa a Jihar Jigawa, ta fara yajin aikin gargadi na makonni biyu saboda abin da ta ce gazawar gwamnatin jihar wajen warware matsalolin da suka shafi ma’aikatan jami’ar.
Yajin aikin ya fara ne da tsakar daren Litinin jiya Litinin, 15 ga Satumba, kamar yadda kungiyar ta sanar a baya. Kungiyar ta ce ta dauki matakin ne bayan ta yi nazarin tattaunawar da ta gudanar da gwamnatin Jigawa.
ASUU-SLUK ta ce ba ta gamsu da tayin da tawagar gwamnatin jihar ta gabatar mata ba. Daga cikin manyan bukatunta akwai a cire jami’ar daga tsarin IPPIS, da kuma biyan bashin karin girma da ake bin wasu ma’aikata tun shekarar 2024.
Kungiyar ta kuma nuna rashin gamsuwa da matsayar gwamnatin jihar kan kashi biyu cikin dari na kudaden da kananan hukumomi ke bayarwa ga jami’o’in jihar.
A cikin sanarwar da shugabannin kungiyar reshen jami’ar suka fitar, sun yi gargadin cewa idan gwamnati ba ta samar da gamsasshiyar mafita ba bayan yajin aikin na gargadi, za su iya tsunduma yajin aiki na gama-gari kuma mara iyaka.
A baya kungiyar ta ba gwamnatin Jigawa wa’adin makonni biyu domin magance matsalolin, amma ta ce har yanzu ba a samu ci gaban da take bukata ba.
