Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Anambra, Nnanna Ama, ya umarci a binciki jami’an ’yan sanda biyo bayan bacewar wani mutum da ake zargi da fashi da makami, wanda aka ce an kama shi aka kai shi ofishin ’yan sanda amma daga bisani yayi layar zana.
Kwamishinan ya umarci a aika wa DPO na ofishin ’yan sanda na 3-3 da wani jami’in DSP takardar tuhuma, yayin da aka fara matakin ladabtarwa kan wani Sufeto.
Mai magana da yawun rundunar, SP Tochukwu Ikenga, ya ce matakin ya biyo bayan wani bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumunta, wanda ke nuna cewa ba a san inda wanda ake zargin yake ba bayan an kai shi ofishin ’yan sandan.
Kwamishinan ya ce zargin na da matukar muhimmanci, kuma zai iya rage mutuncin rundunar ’yan sandan a idon Jama’a.
Ya ce rundunar ba za ta lamunci sakaci, rashin kwarewa ko amfani da mukami ba bisa ka’ida ba wajen karya ka’idojin aikin ’yan sanda.
