Rundunar Sojin Saman Najeriya, NAF, ta fitar da sunayen mutane 25 da suka mutu a hatsarin jirgin saman rundunar da ya faru a jihar Ondo ranar Litinin.
Rundunar ta ce wadanda suka mutu sun hada da ma’aikatan jirgin biyar da fasinjoji 20.
Kakakin rundunar, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya bayyana sunayen mutanen cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu.
Daga cikin ma’aikatan jirgin akwai:
- Squadron Leader MI Aburime – matukin jirgi
- Squadron Leader AP Man-Ugwueje – mataimakin matukin jirgi
- Flight Lieutenant IS Bako – mataimakin matukin jirgi
- Warrant Officer Abubakar A – injiniyan jirgi
- Corporal Uguru HC – injiniyan jirgi
Fasinjojin da suka mutu
- Flight Lieutenant TL Lazarus
- Flight Lieutenant M Akinloye
- Flying Officer IM Adeshina
- Master Warrant Officer Onwuka F
- Master Warrant Officer Matini BA
- Warrant Officer Nuhu FS
- Flight Sergeant James RB
- Flight Sergeant Mohammed AI
- Sergeant Ani AE
- Sergeant Izibenikien SI
- Sergeant Alafuka C
- Sergeant Mbadugha AN
- Lance Corporal Ugwuba FC
- Lance Corporal Eledan GE
- Mrs Ezeh Nneka
- Godstmine Tarabina
- Joy Micheal
- Sunday Micheal
- Ukeme David
- Gideon Omotola
NAF ta ce jirgin, mai lamba NAF 931, ya yi hatsarin ne a yankin Igbokoda na jihar Ondo.
Rundunar ta ce ta fara cikakken bincike domin gano musabbabin hatsarin, yayin da ta mika sakon ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu.
