Mutane huɗu sun samu munanan raunuka bayan wata babbar motar dakon kaya kirar Mack, ɗauke da kwantena mai girman ƙafa 40, ta yi hatsari a yankin First Gate, kan hanyar zuwa Mile 2 a Legas.
Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Legas, LASTMA, ta ce hatsarin ya faru ne bayan motar ta samu matsalar birki, lamarin da ya sa direban ya rasa ikon sarrafa ta.
Rahotanni sun ce motar ta kutsa cikin wata babbar mota ɗauke da kwantena mai ƙafa 20, da wata motar haya kirar T4 mai lamba AAA 723 YF, da kuma babura guda tara.
LASTMA ta ce mutane huɗun da suka jikkata, maza uku da mace ɗaya, sun samu munanan raunuka da suka haɗa da karaya a hannaye da ƙafafu, jami’an hukumar sun ceto su tare da miƙa su ga ’yan sanda na Roro Police Division, waɗanda suka kai su asibiti domin samun kulawar gaggawa.
An kama direban motar Mack da sauran direbobin da ke da hannu a hatsarin, inda aka miƙa su ga ’yan sanda domin gudanar da bincike da kuma ɗaukar matakin da ya dace bisa sakamakon binciken.
