Rundunar ’yan sandan jihar Bauchi ta kama wani matashi mai shekaru 24, Abdulrazak Sale Kundang, wanda ake zargi da hannu a kisan wani mutum mai suna Rilwanu Dauda, mai shekaru 46, a yankin Karofin Madaki da ke birnin Bauchi.
Mai magana da yawun rundunar, SP Nafiu Habib, ya ce an kama Sale ne ranar 5 ga Oktoban 2026, bayan shafe watanni uku yana buya, ya ce an kama shi ne bayan rundunar ta samu sahihin bayanin sirri.
A cewar ’yan sandan, lamarin ya faru ne ranar 5 ga Yulin 2026, inda ake zargin Sale, wanda aka fi sani da Abba Sale Police, da wasu ’yan ƙungiyarsa sun kai wa Rilwanu Dauda hari tare da caka masa wuka.
Rundunar ta ce an garzaya da Dauda zuwa asibitin koyarwa na jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi, amma likita ya tabbatar da rasuwarsa da misalin ƙarfe 11 na safe a wannan rana.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, Sani-Omolori Aliyu, ya umarci a gudanar da cikakken bincike tare da gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu idan binciken ya kammala.
