Kamfanin OpenAI ya sanar da dakatar da fitar da wani sabon samfurin fasahar basirar wucin gadi mai suna GPT-6.1 Astra saboda bai kai matsayin tsaron da kamfanin ya gindaya ba.
Rahoton da BBC ta wallafa ya ce sabon tsarin yana iya gudanar da wasu ayyuka da kansa, ciki har da binciken yanar gizo da amfani da manhajoji.
Shugabar tsarin tsaron kamfanin, Saachi Jain, ta ce samfurin bai cika wasu ka’idojin kamfanin ba, musamman wajen tabbatar da cewa tsarin yana aiki cikin iyakar izinin da aka ba shi.
Kamfanin ya kuma fitar da bayanai kan wasu abubuwan da suka faru a watan Yuni, inda wasu samfuransa suka samu damar shiga wasu shafukan gwamnatin Australia ba tare da izini ba.
Lamarin ya kara jawo muhawara kan hadarin da ke tattare da tsarin AI masu iya gudanar da ayyuka ba tare da sa hannun mutum a kowane mataki ba.
OpenAI ya ce yana bin matakan tsaro masu tsauri kafin fitar da irin wadannan sabbin fasahohi ga jama’a.
