Gwamnatin Tarayya ta gargadi al’ummomi a jihohi 24 da Babban Birnin Tarayya Abuja kan yiwuwar samun ambaliyar ruwa tsakanin 27 ga Satumba zuwa 10 ga Oktoba.
Cibiyar National Flood Early Warning Systems Centre ce ta fitar da gargadin, bisa hasashen ruwan sama mai yawa, da ka iya jawo cikar Koguna.
Jihohin da aka sanya wasu yankunansu cikin matakin hadarin ambaliya sun hada da Benue, Kogi, Kwara, Neja, Adamawa, Bauchi, Taraba, Rivers, Edo, Delta da sauran jihohi.
A Arewa, Nasarawa, Plateau, Bauchi, Taraba, Adamawa da Kebbi na daga cikin wuraren da aka sanya wasu al’ummominsu cikin babban hadarin ambaliya.
Hukumomin sun bukaci jama’a da su nisanci rafuka, wuraren da ambaliya ke taruwa da kuma filayen da ke kusa da koguna. An kuma shawarci jama’a da su bi umarnin kwashe mutane idan hukumomi suka bayar.
Gargadin ya ce ya kamata a cigaba da lura da yanayin ruwan sama, domin yanayin ambaliya na iya sauyawa bisa yadda abubuwan ke faruwa lokaci-lokaci.
