
Aminu Abdullahi Ibrahim
Majalisar Dattawan Najeriya ta dage wani taron koli na tsaro na ƙasa da aka shirya gudanarwa a ranar 12 da 13 ga Oktoba.
An ce dage taron ya biyo bayan hatsarin jirgin Rundunar Sojin Sama da ya kashe mutum 25 a Igbokoda ta Jihar Ondo.
Taron na daga cikin matakan da Majalisar ke shiryawa domin tattauna matsalolin tsaro da hanyoyin inganta yaƙi da ta’addanci da sauran laifukan da ke barazana ga ƙasar.
Dage taron ya ba Majalisar damar mai da hankali kan abin da ya faru da jami’an Sojin Sama da sauran mutanen da ke cikin jirgin.
Hukumomin tsaro sun kuma tabbatar da cewa ana gudanar da bincike domin gano musabbabin hatsarin.
Har yanzu ba a bayyana sabuwar ranar da za a gudanar da taron tsaron ba.
