
Aminu Abdullahi Ibrahim
An kai hare-haren makamai masu linzami kan filin jirgin Aden na ƙasar Yemen yayin da dakarun da ke goyon bayan gwamnatin Yemen ke ƙara matsa wa ’yan Houthi.
Rahotanni sun ce an harba makamai masu linzami biyu zuwa filin jirgin, yayin da aka ce wani makami ya kuma nufi yankin Riyadh na Saudiyya.
Gwamnatin Yemen da ke samun goyon bayan Saudiyya na ƙoƙarin kwato wasu yankunan da Houthi ke iko da su.
Dakarun gwamnatin sun kuma ƙaddamar da farmaki a yankin Taiz, kusa da wasu muhimman wurare da ke da alaƙa da mashigar Bab al-Mandeb.
’Yan Houthi sun musanta wasu daga cikin ikirarin da gwamnatin Yemen ta yi kan nasarorin da ta samu a fagen daga.
Rikicin na da muhimmanci ga tattalin arzikin duniya saboda yankin Bab al-Mandeb na daga cikin muhimman hanyoyin safarar kayayyaki da makamashi tsakanin tekun Red Sea da sauran sassan duniya.
