Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta yi gargadin cewa kungiyar Boko Haram na shirin kai manyan hare-hare a jihohin Adamawa da Borno.
Rahotanni sun nuna cewa gargadin ya shafi karamar hukumar Michika a jihar Adamawa da kuma karamar hukumar Askira-Uba a jihar Borno, inda ake zargin kungiyar ke shirin kai hare-hare.
A cewar rahoton da TheCable ta wallafa, wata sanarwar da hukumar DSS ta bayyana cewa yiwuwar hare-haren na da alaka da rushewar yarjejeniyar tsagaita wuta da ake zargin ta kasance tsakanin ‘yan ta’addan da gwamnatocin jihohin biyu.
Takardar ta kuma ce ‘yan ta’addan na shirin yin garkuwa da wasu manyan jami’an gwamnati, kansiloli, hakimai, shugabannin addinai, da kuma mazauna yankunan da abin ya shafa.
Haka kuma, takardar ta ce ‘yan ta’addan sun riga sun tura wata tawagar leƙen asiri domin shirya kai harin.
Bisa wannan dalili, DSS ta bukaci jami’an tsaro, masu gadin dazuka da sauran hukumomin da abin ya shafa su kara tsaurara matakan tsaro tare da sa ido a yankunan da aka ambata domin dakile duk wata barazana.
Rundunar Sojin Najeriya ta fara bincike kan yadda rahoton sirrin da ke dauke da wannan gargadi ya shiga hannun jama’a.
