
Aminu Abdullahi Ibrahim
Hukumar tsaro ta farin kaya ta DSS ta ce ta fara bincike kan jami’anta da aka gani a wani bidiyo suna jan ɗan gwagwarmaya kuma ɗan siyasa, Omoyele Sowore, daga harabar kotu bayan zaman shari’a a Abuja.
Lamarin ya faru ne bayan wata Babbar Kotun tarayya da ke Abuja ta umarci a tsare Sowore a gidan yarin Kuje har sai an saurari ƙarar da ya shigar yana ƙalubalantar soke belinsa.
Mai Shari’ar Mohammed Umar, ya yanke hukuncin ne bayan ya yi watsi da buƙatar Sowore ta janye kansa daga sauraron shari’ar bisa zargin nuna son kai.
A ranar 16 ga Yuni, kotun ta soke belin da aka ba Sowore tare da bayar da sammacin kama shi bayan ya gaza bayyana a gaban kotu.
Bayan zaman kotun, wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta ya nuna wasu jami’an DSS dauke da makamai suna jan Sowore ta ƙarfi daga harabar kotun.
Bidiyon ya janyo suka daga jama’a da kungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam kan yadda jami’an suka gudanar da aikin.
A martaninta, DSS ta ce ta lura da korafe-korafen da jama’a suka yi kuma ta bayar da umarnin gudanar da bincike domin gano ko jami’an sun bi ƙa’idojin aiki ko kuma sun wuce gona da iri.
