Gwamnan jihar Kebbi Dakta Nasir Idris bukaci rundunar sojin kasar nan ta kawar da ’yan bindiga da ke ci gaba da barazana ga rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin ziyarar ba-zata da ya kai wa sojoji a sansaninsu da ke Yauri, inda ya yaba musu saboda jarumtaka da sadaukarwarsu wajen gudanar da ayyukansu.
Gwamna Dakta Nasir Idris ya sake tabbatar da kudurin gwamnatinsa na samar da dukkanin tallafin da ake bukata da kuma yanayin aiki ga hukumomin tsaro.
Ya ce tsaro nauyin kowa ne, don haka ya bukaci gwamnatocin jihohi su kasance masu ruwa da tsaki wajen tallafa wa gwamnatin tarayya wajen kare al’ummomin dada cikin hadari.
Ya ce hakan zai taimaka wajen samar da yanayin da zai ba manoma damar komawa gonakinsu cikin aminci domin ci gaba da noma.
