Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana damuwa kan yadda cutar Ebola ke cigaba da haddasa mutuwar yara kanana a jamhuriyar Demokradiyyar Congo.
Kakakin Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya, Farhan Haq, ya shaida hakan a taron manema labarai a ranar juma’ar data gabata cewa, yara kanana sama da 300 sun rasa rayukansu tun bayan sake barkewa cutar.
Farhan , ya ce yara ne ke da kaso mafi yawa cikin wadanda suka kamu da cutar kwatankwacin kashi 1/3 na mace macen da ake samu.
Asusun tallafawa yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya yi gargadi kan mumunan tasirin cutar kan tsarin kiwon lafiya inda ya bayyana fargaba a gameda yadda cutar ke yaduwa cikin sauri.
A yankunan da dama inda cutar tafi kamari an samu koma bayan kula da marasa lafiya da kashi 40% a yan watannin nan inji shi.
