Gwamnan Jihar Katsina kuma Shugaban Ƙungiyar gwamnonin arewa maso yamma, Malam Dikko Umar Radda, ya ce gwamnatocin yankin sun ƙudiri aniyar tabbatar da zaman lafiya da ci gaba, tare da tallafa wa al’umma domin inganta rayuwarsu.
Gwamna Radda ya bayyana hakan ne, yayin da ya halarci shirin auren gata da gwamnatin Kano ta shirya ƙarƙashin Hukumar Hisbah ta jihar, inda aka ɗaurawa ma’aurata 1,500 aure.
Gwamnan ya ce gwamnati na da alhakin tallafawa al’umma da inganta jin daɗin su, yana mai bayyana shirin auren gata a matsayin wani mataki na tallafawa iyalai wajen fara rayuwar aure, tare da tabbatarwa da gwamnatin Kano cikakken goyon bayan Ƙungiyar gwamnonin ta arewa maso Yamma ga shirye-shiryen da ke ƙarfafa zaman lafiyar iyalai da jin daɗin al’umma.
A nasa jawabin, Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya ce shirin na auren gata wani ɓangare ne na alkawarin gwamnatinsa na tallafawa iyalai a dukkan ƙananan hukumomi 44 da mazabu 484 na jihar, inda gwamnati ta ware kuɗaɗe domin gudanar da gwaje-gwajen lafiya, tallafin aure da sauran abubuwan jin daɗi ga ma’auratan.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito gwamna Radda na yabawa malamai, sarakunan gargajiya, ’yan kasuwa da sauran masu ruwa da tsaki bisa gudummawar da suke bayarwa wajen jagorantar ma’auratan, yana mai cewa koyarwar malamai kan aure, haƙuri, mutunta juna da ɗaukar nauyin iyali na taimakawa wajen gina ingantattun iyalai.
