Gwamnatin Kano ta fara horar da ma’aikatan kiwon lafiyar dabbobi yadda za su gudanar da rigakafin cututtukan su tare da tattara bayanan masu kiwo ta hanyar amfani da na’urorin zamani.
Da yake kaddamar da horon, kwamishinan ma’aikatar bunƙasa kiwo ta Kano Dr Aliyu Isa Aliyu bayyana cewa shirin zai taimaka wajen samar da sahihan bayanai kan masu kiwo da dabbobinsu a faɗin jihar.
Dr Aliyu ya ce bayanan da za’a tattara sun haɗar da sunan mai kiwo, adireshinsa, yawan dabbobinsa, waɗanda aka yiwa rigakafi da waɗanda ba a yiwa ba, tare da bayyana dalilan hakan domin sauƙaƙa tsara manufofin bunƙasa kiwo.
Kwamshinan ya kara da cewa matakin wani ɓangare ne na ƙoƙarin gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf na zamanantar da harkar kiwo da daidaita ta da tsarukan da ake amfani da su a ƙasashen duniya.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito guda daga cikin mahalarta horon Bashir Garzali El Mahmud na bayyana fatan cewa shirin zai taimaka wajen inganta lafiyar dabbobi, ƙara yawan amfanin kiwo da bunƙasa tattalin arzikin jihar Kano.
