Gwamnatin Kano ta ƙara tsaurara sanya ido da ɗaukar matakan da zasu kawo daidaito akan ayyukan shirin rigakafin zazzabin cizon sauro na shekarar 2026, bayan kammala cikakken binciken tsare-tsare, da shirin ma’aikatan da za su gudanar da aikin.
Hakan ya biyo bayan kammala aikin wani kwamiti na musamman wanda ma’aikatar lafiyar Kano ta kafa tun a ranar Laraba, 5 ga watan Agusta, 2026, domin gudanar da bincike kan tsare-tsare da shirye-shiryen da ke ƙunshe a cikin shirin rigakafin zazzabin cizon sauron na lokacin damina
Da yake yiwa Premier radio karin bayani, jagoran kwamitin kuma shugaban Hukumar yaƙi da yaɗuwar cutar Kanjamau ta Kano Dr Usman Bashir, ya ce kwamitin yayi binciken sa ne kan yadda aka shirya aikin, hanyoyin gudanar da shi, rarraba magunguna da kuma yadda ake aiwatar da shi a faɗin Kano, da tattaunawa da jami’an shirin daga ƙananan hukumomi 44, domin daidaita bayanan shirin na kowace ƙaramar hukuma.
Dr Bashir ya ce an ɗauki matakan ƙara inganta tsarin ta hanyar sanya ido, yayin da aka naɗa Abdullahi Yusuf Koki a matsayin Mukaddashin Manajan Shirin, da Bashir Maikano a matsayin Mukaddashin Jami’in Sa’Ido da tantancewa na jiha, yayin da Surayya Aminu ta zama Mukaddashiyar Mataimakiyar Jami’ar Sa’Ido da tantancewa ta jiha, tare da tura jami’ai uku daga Hukumar kula da lafiya a matakin farko domin ƙara ƙarfafa aikin tantancewa, daidaitawa da sa’ido a sassan Kani.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Dr Bashir na cewa da zarar sun kammala tantance sauran shirye-shiryen da suka dace, za a fara gudanar da shirin rigakafin zazzabin cizon sauro na shekarar 2026 a faɗin Kano ranar laraba, 12 ga watan Agusta, yayin da kwamitin binciken zai ci gaba da aikinsa tare da gabatar da cikakken rahoto da shawarwari, ciki har da matakan gyara da na ladabtarwa ko hukunci ga duk wanda aka samu da laifi.
