Gwamnatin Kano ta horar da kungiyoyin malaman Da’awa 70 hanyoyin amfani da fasahar zamani ta Artificial Intelligence (AI) wajen isar da saƙon addinin Musulunci cikin sauƙi da inganci.
An gudanar da horon ne ƙarƙashin jagorancin Hukumar Shari’a ta Jihar Kano, wadda ta shirya taron bita ga ƙungiyoyin Da’awa mai taken Tasirin Haɗin Kan Ƙungiyoyin Da’awa Wajen Yaɗa Addinin Musulunci.
Da yake gabatar da Maƙala mai taken “Salon Isar da Da’awa Ta Kafafen Sadarwa,” Malam Garba Umar Fagge ya ce amfani da fasahar AI zai taimaka wajen sauƙaƙa hanyoyin wa’azi da yaɗa saƙon addinin Musulunci, tare da ba da damar isar da saƙon ga al’ummomi a sassa daban-daban na duniya.
Tun da farko, da yake jawabi Shugaban Hukumar Shari’a ta Kano, Sheikh Abbas Abubakar Daneji, ya ce gwamnatin jihar ta shirya bitar ne domin bai wa malaman Da’awa damar fahimtar wasu sabbin hanyoyin gudanar da ayyukansu, da kuma ƙarin sanin tanade-tanaden kundin tsarin mulki da suka shafi ayyukan Da’awa.
Shi ma Kwamishina na Biyu a Hukumar Shari’a, Sheikh Ali Danabba, ya jaddada muhimmancin amfani da hanyoyin zamani wajen isar da saƙon Da’awa.
A nasa ɓangaren, Barrister Ibrahim Sule, wanda shima ya gabatar da Maƙala mai taken kiyaye doka ta Hanyar yin da’awa, ya yi kira ga malaman Da’awa da su tabbatar da bin dokokin ƙasa da ƙa’idojin da suka shafi yaɗa saƙon addini.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito cewa taron ya samu halartar Shugaban Hukumar Shari’a, Sheikh Abbas Abubakar Daneji, Kwamishinonin Hukumar na ɗaya da na biyu, Gwani Hadi da Sheikh Ali Danabba, da kuma shugabannin ƙungiyoyin Da’awa da ke gudanar da ayyukansu a faɗin Jihar Kano.
