Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya jinjinawa sarakunan gargajiya, malaman addinin Musulunci, gwamnonin jihohin arewa maso yamma da sauran manyan baki, BISA irin gudunmawar da suka bayar wajen tabbatar gudanar da shirin ɗaura auren gata na jihar cikin nasara.
Gwamna Yusuf ya bayyana godiyarsa musamman ga shugaban Majalisar Sarakunan Kano da sarakunan Kano, Rano, Karaye da Gaya, saboda shawarwari, addu’o’i da gudunmawar da suka bayar wajen gudanar da bikin.
Gwamnan ya kuma jinjinawa malaman addinin Musulunci da suka zo daga sassa daban-daban na Najeriya domin halartar bikin, yana mai cewa addu’o’i da shawarwarin da suka bayar sun taimaka matuka wajen samun nasarar shirin.
Haka kuma, Gwamna Yusuf ya godewa takwarorinsa na jihohin arewa maso Yamma, ciki har da Gwamnan Katsina, Umar Dikko Radda, da Gwamnan Jigawa, Umar Namadi, da Gwamnan Kebbi, Dakta Nasir Idris, da kuma wakilan wasu gwamnonin, bisa halartar bikin da nuna goyon baya ga shirin.
Ya kuma yaba wa shugabanci da ma’aikatan Hukumar Hisbah ta Kano, ƙarƙashin jagorancin Kwamandan-Janar, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, saboda jajircewarsu wajen tabbatar da ɗabi’un kirki, zaman lafiya da walwalar al’umma.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Gwamnan na kuma miƙa godiyarsa ga ‘yan kasuwa, jami’an diflomasiyya, ƙungiyoyin farar hula, abokan hulɗar ci gaba da sauran baƙi da suka halarci bikin ko kuma suka aike da saƙonnin fatan alheri.
